19 Maris 2021 - 16:31
Shugaban Kasar Iraki Ya Jaddada Matakin Da Majalisar Kasar Ta Dauka Na Fitar Da Sojojin Amurka Daga Kasar

Shugaban na kasar Iraki Barham Salih ya fada a jiya Alhamis cewa; A halin yanzu sojojin Amurka da wasu na kasashen waje a cikin kasar ba su wuce 2,500 ba, kuma ba da jimawa ba zamansu a cikin kasar zai zo karshe.

ABNA24 : Shugaban kasar ta Iraki ya kuma yi ishara da sabanin da ake da shi a tsakanin Bagadaza da Arbil,tare da jaddada wajabcin fito da hanyoyin dinke Baraka.

Tun bayan kisan gillar da Amurka ta yi wa Janar Kassim Sulaimani da Abu Mahadi Muhamdi, al’ummar Iraki suke yin kira da a kori sojojin Amurka daga kasar.

Majalisar kasar Irakin ta yi kuduri wanda ya bukaci sojojin Amurkan da su fice daga kasar.

342/